A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah al-Uzma Jafar Subhani shi ne ya jagoranci sallar jana'izar Shahidin Jagora, Ayatullah al-Uzma Shahid Sayyid Ali Hussaini Khamenei (Q) tare da wasu daga cikin iyalansa wadda aka gudanar yau Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026 a masallacin juma'ar birnin Tehran. Jana'izar dai ta samu halartar miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na cikin ƙasar Iran da ma ƙetare.
Ayatullah Shahid Sayyid Ali Hussaini Khamenei dai ya yi shahada ne a gidansa a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 sakamakon harin ta'addancin da gwamnatin Amurka da haɗin gwiwar yar koronta Isra'ila suka kawowa jamhuriyar Musulunci ta Iran.



Ra'ayinka